Thursday, October 30, 2008

"Tunanin Gwarzo"

Zakariyya Muhammad Sarki

Tun wajen asuba aka fara ruwan sama, duk da cewa kuma ya dan tsagaita har yanzu da safiya ta yi ba a dena ba. Ruwa ne da aka yi da yawa kamar da bakin kwarya. Gwarzo na tsaye yana kallon zubowar ruwan ta tagar dakinsa. Kasancewar ba shi da lema ko rigar ruwa, burinsa shine ruwan ya tsagaita domin ya fita zuwa cikin birni inda yake sa ran halartar wata ganawa ta tantacewar daukar aiki, wato ‘interview’. Yayin da agogo bai dena motsawa, Gwarzo na cikin damuwa domin wannan ba karamar dama bace a wajensa, damar da yake ganin zata yanke masa bakar wahalar da ya dade ya na sha ta neman aiki. Domin duk da cewa ya kammala karatunsa na digiri ba tare da wata matsala ba, aiki ya riga ya fi karfinsa; ya yi ta neman aiki tun kusan shekara biyu kenan amma bai samu ba. Ya yi yawo daga wannan kamfani zuwa wancan, daga wannan ma’aikatar gwamnati zuwa waccan, amma shiru ka ke ji, “No vacancy” shine abinda yake karantawa a mafi yawan kofofin kamfaninnukan da yake zuwa. Ma’ana basa bukatar ma’aikaci. Ma’aikatun gwamnatin kuwa duk inda ya je sai ace masa ya tafi Hukumar Daukar Ma’aikata ya bada takardunsa. Ko yaushe za su dauke shi? Wasiku kuma na neman aiki shi dai ba zai iya tuna yawan wanda ya rubuta ba. Maganar dai kullum daya ce. “No vacancy.” Farko yayi tunanin ko dai baki aka yi masa ne ko kuma dai takardun sa ne basu yi kyau ba domin wahalar ta kai wahala, amma ganin wasu masu takardun da basu kai ma nasa ba sun samu aiki, sai ya canza tunanin sa, ya yarda cewa akwai abin bincike, ta yiwu akwai wani sirri na samun aiki da shi bai sani ba. To amma wane sirri ne? Yaya kuma haka za ta rika kasancewa? Wani abokinsa da suke tare da shi mai suna Danbirni ya bashi amsa.
“Ai abu ne mai sauki mutum ya samu aiki yanzu! Ba ka bukatar takardun makaranta!”
“Kamar yaya?”, cike da mamakin abinda ya fada Gwarzo ya tambayi abokinsa.
Abokin nasa na wata irin dariya ta shakiyanci yace, “Malam, ai abun da kawai ka ke da bukata shine ka shafe yatsun hannun masu daukar ka aiki da mai ko kuma ka sosa musu bayansu, sai kawai su dauke ka!”
“In shafe yatsu, in sosa baya, kamar yaya?”. Yaren ya kasance bako a wajen Gwarzo.
“Eh, yanzu shi ake yayi a manyan biranen kasar nan, kai har ma kowane gari da kowane wuri: a makarantu, a kotuna, a ofishin yan sanda, a wajen kasuwanci…duk inda dai zaka iya tunani haka abin yake. Dole ka bada kafin a baka.”
Wannan labari ya bawa Gwarzo matukar mamaki, kasancewarsa dan kauye wanda in ban da albarkacin karatun jami’a bai taba dandana rayuwar birni ba.
A tsaye yake yana kallon ruwan da ya tsare shi a gidan abokinsa Danbirni, yayin da lokacin ganawar ke kara matsowa, zuciyarsa kuma na bugawa da sauri yana tsoron dalilin da zai sa ya rasa wannan dama ta daukar aiki. Duk da dai cewa bai gama amincewa da ya fara bin sahun yan birni ba, ba kuma zai yadda da abin da zai sa yayi asarar aikin nan ba. Danbirni ya yi nasarar cusa masa wannan banzan ra’ayi ko hanya ta ‘sai ka ba ni zan baka.’
“Abokina! Idan kana so ka yi nasara dole ne ka dan rika…ganinsu…ka dai gane. Idan ka ce za ka yi gaskiya ko kuma wai ka nuna musu takarda, to ko kai ne mangwafak ba za ka taba samun biyan bukata ba,” Danbirni ya ce masa. “Kalle ni, na samu abinda ka ke gani na da shi din nan ne saboda na san dawan garin. Takun da ake yayi ke nan yanzu.”
Duba ya zuwa abin da Danbirni ya ke da shi na lafiyayyen aiki, dan gidansa mai kyau da kuma motarsa ta hawa ga shi kuma bai kai shi yawa ko kyan takardu ba ya sanya Gwarzo yadda da abinda Danbirnin ya fada masa.
Saura kamar awa daya a fara ganawar tattancewar, don haka ba zai iya jurewa ya jira tsagaitawar ruwan sama ba. Sai kawai ya fita ya dauki hanya, kwalin digirinsa na makale a jikinsa; da dukan talauci ai gwamma na ruwa. Yana tafiya yana zargin irin al’ummar da ya tsinci kan sa a ciki, al’ummar da ta bar mutane irinsa na shan wahala a dalilin cin hanci da tsantar rashin adalci. To amma me yasa ya san da haka ya yarda igiyar ruwan ta tafi da shi? Rayuwa! Eh mana, dole ya rayu; to amma dole ne ya sayi rayuwar, domin ta Allah ce?
Ga shi dai yanzu har ya isa cikin gari a mintuna kasa da talatin, lallai ya yi sa’a. Ya jike sharkaf sai dai kuma cike yake da murna, domin nan da mintuna talatin zai samu aiki cikin sauki kamar yadda Danbirni ya tsara masa.
“Abu ne mai sauki abokina, dunkule ne na yan dubu-dubu za su yi abin mamakin.” Wadannan kalmomin ne ke kai kawo a zuciyarsa. Sai ya yi murmushi domin Danbirni ya ranta masa kudin da zai amfani da su wajen wannan ‘kasuwanci’. Kai sai da ta kai ma Danbirni ya yi wa jami’in daukar aikin waya domin ganin komai ya tafi dai-dai. Ka ji dan gari!
“Mutumen yana da kirki, ya na son ya ga matasa sun samu aiki!” Danbirni ya fadawa Gwarzo lokacin da ya ke ba shi kudin. “Wadannan yan kudin na iya tausa shi, komai ya tafi dai-dai. Za kuma ka ga abinda nake nufi, ai kamar ka samu aiki ne abokina.”
Gwarzo ya yiwa kansa da kansa murmushi don sauran yan mitoci tsakaninsa da wajen da yake ganin nan ne madafar sa kuma mayankar wahalarsa ta karshe. A yanzu ma dai ga shi har ya karaso dai-dai ginin ma’aikatar. Ya duba titi ya tsallaka, ya ci gaba da ratsa motocin da aka ajiye har ya isa bakin ginin. Yanzu sauran minti biyar tsakaninsa da sabon aikinsa da zai fara! Sai ya kara kintsawa ya dan gyara jikinsa, ya danna kai cikin kofar ma’aikatar.
“Tabdijan!” Gwarzo ya fada yayin da ya ga tarin mutanen da suke sa ran a gana da su domin a dauke su aikin. “Yanzu a hakan za’a dauke ni a bar duk wadannan mutanen.” Gwarzo ya fada yana mai shakku. “Haba! Dauka? Ai an ma dauke ka, kar fa ka manta da irin takun da kake yi, taku ne da ba shi da marasa nasara. Matukar ka yi shi ka samu nasara.” Wani bangare na zuciyarsa ya kara tunatar da shi tare da karfafa masa gwiwa.
“Barkan ku da zuwa, maza da mata, duk wanda ya zo domin a dauke shi a matsayin Mai kula da jin dadin ma’aikata ya biyo ni,” wata mata mai matskaicin shekaru ta fadawa taron masu neman aikin, ciki har da Gwarzo. Sai Gwarzo da wasu mutum shida suka bi ta.
Mista Katako Dangari, wani mutum mai babban kai da mummunar kama mai kuma bakin baki a dalilin tsananin shan sigari, na zaune a kan kujerarsa yana jujjuyawa yana jiran wadanda zai tantance. Ka ji dangari, tattance aiki shi kadai! A gabansa kuma a kan teburinsa ga takarda dauke da sunayen wadanda za’a gana da su. Daya bayan daya masu neman aikin suka rika shiga. Daga karshe kuma sai Gwarzo. Kayan jikinsa a jike su ke, amma dai ya goge fuskarsa. Shigarsa ke da wuya sai Dangari ya mike ya tarbe shi.
“Sunana Katako Dangari, Shugaban Sashen Lura da Ma’aikata,” haka ya fada yayin da ya mikawa Gwarzo hannu. Dangari Ya nunawa Gwarzo kujera ya ce masa ya zauna. Bayan Gwarzo ya zauna sai Dangari ya kalli idanuwan sa ya ce, “Yauwa, ina fata ka zo da ‘man’ ko? Don na san ka rigaya ka san komai.”
“Eh…eh, yallabai na zo da su,” yayin da ya sa hannunsa yana yar’ makyarkyata zai fito da ‘mai’ daga cikin aljihu! Zuciyarsa ta yi wani dar, aljhunsa ba komai, ba kudi ba dalilunsu. To me ya faru da su? Ko dai sun zube ne garin sauri ya riski lokaci? Can sai ya tuna ashe ya bar su ne akan wani dan teburi a can gidan abokinsa.
“Yallabai, na…na manto man,” Gwarzo ya fada yana mai kaduwa.
“To sai me kenan? Na san dai Danbirni fada ma duk yadda abin ya ke, ko bai fada ma ba?”
“Eh, ya fada mini, amma ina da digiri di na a nan… ina nufin takardu na duk ga su nan.”
“Digiri? Ai duk wadanda ka ga sun shigo nan kafin ka shigo su ma su na da digirin. Ka ga malam, ka cika alkawari in kuma ba haka…”
Gwarzo ya duba irin nisan da gidan abokinsa ya ke da shi idan har komawa zai yi. Anya kuwa za’a jira shi ya je ya dauko domin tuni wasu sun zo da na su man, ta yiwu ma na shanu, ga kuma rashin kyawon yanayi saboda ruwan sama da har yanzu bai gama tsayawa ba.
“Don Allah ka taimake ni, ka rufa mini asiri. Na sha matukar wahala”, Gwarzo ya roki Dangari.
Ya yi murmushi ya dan zuke wata yar guntuwar taba da yake sha sannan Katako Dangari yace, “Yaro saurara ka ji, babu fa wani abu yanzu da zaka same shi a banza a wannan zamanin. Duk wadancan da ka gani a waje suna son wannan aikin ne da kai ma kake so, kowa kuma ya yi ‘abinda ya kamata’ ka ga kuwa idan aka dauke ka haka siddan ba tare da ka yi wani abu ba, ai ba a yi musu adalci ba. A gaskiya bai kamata mutum iri na yayi rashin adalci irin wannan ba. Don haka dole ne ka jika mini hannuna ko ka sosa min baya na idan har kana son aiki. Wannan gama garin abu ne ba wai ni kadai ne na ke yi ba.”
Rike da kwalinsa na digiri, hannun Gwarzo ya fara karkarwa. Karkarwar da hannun na sa kuma ke yi sai yake jin kamar aikin ne ke subucewa daga hannunsa, duk dai a dalilin matsala ta cin hanci da rashin adalci. Gumi ya ci gaba da keto masa kamar an watsa masa ruwa. “Gama garin abu ne?” Wace irin lalacewa mu ka yi har wannan abu ya zama gama gari? Ina addini da kyawawar tarbiyya ta al’ada da muke da ita? Ko dai an yi watsi da su? To wai al’umma ma na da bukatar mutane irin su Katako Dangari? Mutanen da suka maida wariya da nuna bambanci tsakanin yan’ kasa daya abun ado, masu ganin cin hanci dai-dai yake da rayuwar su, masu hana ruwa gudu, ma su cutar talakawan kasa, masu tsananin son kan su? “A’a! a’a. Al’umma ba ta bukatar irin su. Lallai ba ma bukatar su!!!”
A hankali a hankali takardunsa suka subuce daga hannunsa suka fadi kasa a dalilin halin da ya shiga. Su na gama faduwa daga hannunsa sai ya mike daga kan kujerar da yake kai yana cije bakinsa yana kara matsawa kusa da Dangari. Ya shiga wani tunani daban.
“Allah ya tsine maka, marar kishi da imani, mugu, kuna cutar kasa da yan’kasa” Gwarzo ya fara fada cikin fushi bayan ya makure wuyan Dangari! “Mutane na can a gari suna ta shan wahala saboda rashin kirkin da kuke aikatawa, saboda ba ku da tausayi da tunanin lahira. Allah wadaran irin ku.”
Dangari tuni ya rikice ya cika da tsoro, idonsa ya rena fata. Kafin ka ce me ji kake ‘kum’ Gwarzo ya yi masa karo a goshi da fuskarsa, ya hada masa jinni da majina. Sai gogan naka ya fadi rikica, da ma yawancin irin su ba karfi gare su ba. Ko cikakken kara gogan naka ya kasa yi.
Ganin haka sai Gwarzo ya tattara takardunsa ya fice daga ofis din. A waje kuma ga mutane na jira su ji waye kuma zai shiga bayan Gwarzon ya fito. Shi dai bai yiwa kowa Magana ba, ya yi ficewar sa yana mai jin dadi da alfahrin abinda ya yi. “Alhamdu lillahi, abu ya yi kyau, wannan shine farkon yakin da na shirya da rashawa, da cin hanci da kuma duk sauran rashin adalci. Na kuma godewa Allah da ya sa har na shiga na fito bai bani iko na bi sahu ba. Da yardar Allah kuma na yi alkawari ba zan kara shiga ba.” Gwarzo ya ke tuntuntuni da fada a zuciyarsa yayin da yake ficewa daga ma’aikatar.