Monday, December 3, 2007

SHIN-“BLUE-FIM” MARYAM HIYANA TAYI?
Daga Danjuma Katsina
Labarin bakin ciki da takaici ya cika duniyar Hausawa a satin da ya wuce na Labarin wata yarinya da tayi abin da aka kira “blue fim” watau fim na batsa akan yadda ake saduwa da diya mace.
Labarin yazo ma hausawa da masoya fina-finan hausa kwatsam kuma da ba mamaki koda yake wasunmu da suke bin diddogin yadda yan fim ke harkarsu sun dade da sanin jita-jitar, wasu suma suna da di-din abin yi faru. Duk wanda yaga labarin ko kuma yaji abin da ya faru, yakan dira akan wadanda suka aikata aika-aikan.
Musamman zantuka masu zafi sun fi yawa akan yarinyar wadda ita ta shahara sosai kuma tana cikin yan fim na Hausa a yanzu wadanda suke tashen gaske.
Mafi yawan masu magana sun fi tofin Allah tsine akan Maryam da zantuka marasa dadin jin a gare ka.
Na karanta wata jarida ma tace wata hukuma ta zartarma da Maryam hukuncin kisa da jefewa.. Yayin da ake ta wannan takaici da kuma juyayi akan abin bakin ciki hoto irin wannan ya fito daga hausa Fulani kuma musulma. Ni inaso ne inyi nazari a mahangar dalilin da ya akayi, haka in kuma yi wasu yan tambayoyi.
Ma’anar “Blue fim” shine fim ne da akanyi domin nishadantarwa ga masu kallo ya tada masu kaimi su biya bukatarsu a lokacin da suke saduwa da mata.
Kamfanonin yin wadannan fina-finai suna da yawa a turai da Amurka wadanda ana yinsu ne, domin a sayar a ci riba.
Masu yin wadannan suna da rijistasu suna kuma da lasin na yin abinsu akan suyi su sayar su kuma watsa shi.
Suna nuna yadda ake saduwa da mace a ta si gogi da yawa da kuma irin motsin da mace zatayi ko na miji ya gamsar da abokin yin sa.
“Blue fim” kala kala ne akwai na maza da mata, akwai na mata da mata (madigo) da na maza da maza (luwadi) da lalacewar ta kara yawa har ma aka koma anayin na dabbobi da mutane da na dabbobi da dabbobi.
“Blue fim” fim ne da aka shirya domin kasuwanci da nishadantar ga mai kallo, malam nan masulmici baki dayansu, na duk mazhabobin duniya suna haramta yin “Blue fim” da kuma kallonsa.
Don haka yinsa da kallonsa baya da gurbi acikin addinin Musulunci HARAM-HARAM-HARAM. Daga abin da ake nunawa na abin da Maryam Hiyana tayi, shin “blue fim” ne tayi?
Tayi abin da tayi ne domin a watsa a sayar ta sami kudi? ko-ko wanda ya dauketa biyanta yayi ya kuma yi yarjejeniya da ita akan watsa shi duniya ta gani yaci riba daga kudin da na biya ta?
Na kalli abin da idona na ma yi ta mai dashi baya yana dawowa domin gano abin da zan iya fito dashi domin wannan rubutu. hoton ma motsawa yana da tsawon minti takwas da sakan talatin da shidda.
Hoton ya fara ne da maryam na kwance tsirara haihuwar uwarta mai dauka, yana dauka muryam na cewa ki taso mana. Tana fadin a’a bani tasowa yana fadin kunya me ki ke ji? tana magana baka jin zancenta.
Da ya matsa sai ta jawo zani ta rufe jikinta sai ya ce gaba da ki taso mana kiyi rawa, tana fadin banyi yana cewa baki yin rawar?
Daga nan sai ya rika ce mata ya kunyar, me zaki ji mu kadai ne fa da ni sai ke sai ya haska “kamera” a jikinsa yana cewa kalli ni ma ina na dau kai na. Sai aka nuna shi tsirara haihuwar uwarsa yana wasa da azzakarinsa.
Daga nan sai ya nufo ya hau bisa ruwan cikinta ya rike kemarar da hannu daya yana daukarsu suna a bisa gado.
Daga baya sai ya koma ya dauka farjinta da sauran jikinta karshe ko lura tayi abin yayi yawa? sai ya tawo bargo da ta rufe jikinta
Duk wanda yaga abin ya san cewa lallai maryam ta sani ake wannan daukar amma kuma duk wanda yaga fuskarta da yanayinta ya tabbatar da cewa ba da so ta ake daukar ba.
Duk wanda yake jin maganganun mai daukar zai san cewa da wata manufa ya ke daukar na ta, da niya a tare dashi.
Yana kokarin ya dauko fuskarta domin wanda zai gani ya tabbatar itace yana kokarin daukar duk tsaraicinta domin gama mata illa baki dayanta.
Mai magana yana kokarin kalallame ta da zance domin ta gamsu akan cewa nishadi ne kawai suke yi a tsakaninsa.
Duk wanda yayi nazarin hoton zai iya kawo abubuwan ukku ga mai daukar. ko dai wani ya sanya shi, yayi ma maryam haka, domin ya sami hoton ya cimma wata bukata tashi, waya sanya shi waya yakema aiki wannan binciken ne zai tabbatar dashi.
Kila kuma wani na son ta, wanda mai dukar yake son, ya bata su, yana ganin wannan itace kawai hanyar da zai iya bi. Ko ta ta ba yi masa wani abu wanda yake ganin cewa abin da kawai zai iya yi ya rama shine ya yi mata wannan ta’addanci don haka ya lallame ta ya kuma yi mata abin da yayi.
Duk wanda yaga hotunan din ya san lallai da niyya akayi shi, wata tsinanniyar niyya da mai yi kawai ya santa da kuma manufar da ya ke.son cimmawa.
Duk wanda ya ga yadda maryam ke jin kunya da ana daukan ta, zai iya kallon kila cikin dalilan da yasa ta kyale ya ke mata wannan cin mutunci
Ko dai tan mugun sonsa wanda take ganin babu yadda za’ayi ya cutar da ita kuma domin ta nuna masa lallai tana son na sa ta bari ta kyale shi, yayi abin abin da yayi
Kowa ya san yadda idan san mace akan mutum ya yi kamari tana iya sallama masa komai na rayuwarta, ko kuma ta na son wani abu a wajensa wanda take ganin sai in ta kyale shi yayi duk abin da yaga dama ita zata iya samun wannan abu ko wata manufa da ta ke son ta cimmawa a rayuwarta akansa wanda mutum na da wannan tunani har ma ya kan ce ranar huce takaici cire kai ba wata tsiya bace.
Wata tambaya mai muhimmanci a lamarin na sune, shine waya watsa hotunan? wa ye sanya shi a yanar gizo har ya, kanun take kamar haka? SIRRIN MARYAM HIYANA?
Wanda daga jin yadda sanya taken yake wani ne ke son watsa ta a duniya! waye wannan? tabbas maryam tayi abin da ya kamata shara’a ta Musulunci wadda daular musulmi ke jago ranta karkashin shugaban na Allah ta ladabtar da ita.ta aikata assha da abin kyama
Kuma duk wani mutumin kwarai dole takaicin abin ya dame shi. Sanar da abin da suka yi a duniya domin kanda garki da jawo hankali da nasiha yana da nasa fa’idar da kuma fadakar don a guje shi hankali.
Amma, me ye amfani yada shi domin nishadi kamar yadda ake yawo dashi a waya?shi kuma mai yio, menene matsayinsa a shara’a da kuma daratta rayuwar Dan’Adam. Dole ne, a fi maganar Maryam tun da yar fim ce, kuma tayi suna.
Amma me ya sa a tofin tsinuwar ba’ayi akan wanda ya yaudareta ya huremata kunne ya kunno bala in? hukuncinsu daya ne! ko nata yafi nasa?
Me yasa yan-jarida da marubuta ba su yi zurfin binciken waye wannan mutum ba kuma me yasa yayi mata haka ba? Mutane sun fi yanke hukuncin akan maryam, shi wannan katon banza me ya hukuncin sa yake?
Zancen gaskiya akwai rashin adalci daga yadda ake rabon laifi da tsinuwa a tsakanin Maryam da fasikin nan wanda suka yi ashsha din a tare.
Masu bin duniyar fina-finan hausa ba zasu taba yafe ma yan-jaridun da marubuta fina-finan hausa ba, har sai sun basu amsar wadannan tambayoyin?
a. Waye wannan fasikin da ya dau hoton Maryam tarihinsa da cikakken adireshinsa da inda yake da abin da yake yi yanzu, da hotunansa kala kala wanda duk inda ka gansa zaka gane shi ka sanshi cewa shine yayi abin da yayi.
b. Waya fito da Hotunan wa ya sanyasu a yanar gizo? da wace manufa yayi wannan?
Wasu tambayoyi kuma yawo sune:
a. Shin so ake a sadaukar da rayuwar maryam duniya da lahira ko-ko so nake tayi nadama ta tsira gobe kiyama? wani mataki za’a iya dauka domin jeji da bala in baya ta funskanci gaba?
b. Shin, in yanzu maryam ta koma ma Allah tsantsa tayi nadama, ko zata iya samun gafarar Ubangiji idan ta maida kanta tsantsa baki daya ga Allah, ko zata iya samun rabo gaban Allah fiye da masu yawo da sunanta domin batanci?
wani hadisin manzo (SAW) yana cewa “zunubi shu’umin abu ne, idan wani nayi kai masa dariya ana iya jarabbat ka dashi.
DANJUMA KATSINA
MARUBUCI NE A JARIDAR
AL-MIZAN

Tuesday, June 26, 2007

DALILIN HALITTAR DAN ADAM

Kafin mu san dalilin halittar dan adam zai yi kyau mu san wanene dan adam din tukuna, akalla dai a takaice. Shi dai dan adam daya ne daga cikin miliyoyin halittu na Allah (SWT). Sai dai duk da kasancewarsa daya daga cikin miliyoyi, ya zama halitta mafificiya a cikinsu, ta inda ku san duk haliitun Allah (SWT) an halicce su ne saboda dan adam din. Za ka iya fahimtar wannan fifiko na dan adam idan ka yi la'akari da matsayai da kuma baye-baye da Allah (SWT) yayi wa dan adam din shi kadai.

Misali, dan adam ne kadai a cikin lamarin halittarsa, duk da cewa ba shi kadai ba ne halitta mai rai, Allah (SWT) ke cewa yayi busa daga ruhinSA a cikin halittarsa. Ya kuma kaddara cewa mafificin dan adam yafi mafificin mala'ika duk da cewa su mala'iku basa taba saba umarnin mahaliccinsu. Dan adam ne dai kadai ya samu matsayi na zama wakilin Allah (SWT) madaukakin Sarki a bayan kasa har ma Allah (SWT) ke aiko manzonni daga cikinsu, duk da cewa ga mala'iku. Wannan ma wani fifiko ne. Hakanan dan adam ne kadai Allah (SWT) ya ba shi damar yankawa da ci da kuma kashe wasu dabbobi, duk da cewa su ma halittu ne, domin kawai ya samu jin dadi da kwanciyar hankali a rayuwarsa. Dan adam ne dai... Hakika baiwar da Allah (SWT) yayi wa dan adam ba ta kirguwa. To, idan ko hakane, halittar dan adam ba zata yiwu ta kasance kamar ta sauran halittu ba. Lallai halittar dan adam tafi karfin wasa. Allah (SWT) na cewa "Kuna zato mun halicce ku ne da wasa, sa'an nan kuma ba zaku dawo izuwa gare mu ba (?)".

Wannan shi zai kaimu ga kokarin amsa tambayar da muka yi tun farko, wato menene dalilin halittar dan adam, tun da ba don wasa aka halicce shi ba? Amsar wannan na cikin Kur'ani mai girma inda Allah (SWT) ke cewa "Ban halicci aljanu da mutane ba sai donkawai su bauta mini..."(51:56). Wannan ke nuna mana cewa dalilin halittar dan adam shine don ya bautawa Allah (SWT) ne kadai.

To menene bautar Allah (SWT)? Mutane da dama na daukar cewa bautar Allah (SWT) shine kayi sallah da zakka da azumi da kuma hajji. Wannan haka yake, amma ba wai bauta ta takaita da wadannan abubuwa ba ne; sun dai kasance ginshikai ne kurum. Saboda haka, bauta a iya cewa aikata wadannan abubuwa ne (ginshikai) kamar yadda Allah (SWT) yace da kuma tafikar da dukkan sauran al'amuran rayuwa cikin lura da horo da kuma hani na Allah (SWT). Domin idan muka diba wadannan ginshikai na bauta suna da kayyadajjen lokaci da ake yin su. Kaga kenan idan aka takaita ma'anar bauta da aikata su kadai zai zamana kamar waccan aya dake maganar bauta ba'a fahimce ta ba, tunda abinda take nunawa babu wani lokaci da dan'adam zai kasance (ya wajaba ya kasance) ba karkashin bautar Allah (SWT) yake ba.