Tuesday, June 26, 2007

DALILIN HALITTAR DAN ADAM

Kafin mu san dalilin halittar dan adam zai yi kyau mu san wanene dan adam din tukuna, akalla dai a takaice. Shi dai dan adam daya ne daga cikin miliyoyin halittu na Allah (SWT). Sai dai duk da kasancewarsa daya daga cikin miliyoyi, ya zama halitta mafificiya a cikinsu, ta inda ku san duk haliitun Allah (SWT) an halicce su ne saboda dan adam din. Za ka iya fahimtar wannan fifiko na dan adam idan ka yi la'akari da matsayai da kuma baye-baye da Allah (SWT) yayi wa dan adam din shi kadai.

Misali, dan adam ne kadai a cikin lamarin halittarsa, duk da cewa ba shi kadai ba ne halitta mai rai, Allah (SWT) ke cewa yayi busa daga ruhinSA a cikin halittarsa. Ya kuma kaddara cewa mafificin dan adam yafi mafificin mala'ika duk da cewa su mala'iku basa taba saba umarnin mahaliccinsu. Dan adam ne dai kadai ya samu matsayi na zama wakilin Allah (SWT) madaukakin Sarki a bayan kasa har ma Allah (SWT) ke aiko manzonni daga cikinsu, duk da cewa ga mala'iku. Wannan ma wani fifiko ne. Hakanan dan adam ne kadai Allah (SWT) ya ba shi damar yankawa da ci da kuma kashe wasu dabbobi, duk da cewa su ma halittu ne, domin kawai ya samu jin dadi da kwanciyar hankali a rayuwarsa. Dan adam ne dai... Hakika baiwar da Allah (SWT) yayi wa dan adam ba ta kirguwa. To, idan ko hakane, halittar dan adam ba zata yiwu ta kasance kamar ta sauran halittu ba. Lallai halittar dan adam tafi karfin wasa. Allah (SWT) na cewa "Kuna zato mun halicce ku ne da wasa, sa'an nan kuma ba zaku dawo izuwa gare mu ba (?)".

Wannan shi zai kaimu ga kokarin amsa tambayar da muka yi tun farko, wato menene dalilin halittar dan adam, tun da ba don wasa aka halicce shi ba? Amsar wannan na cikin Kur'ani mai girma inda Allah (SWT) ke cewa "Ban halicci aljanu da mutane ba sai donkawai su bauta mini..."(51:56). Wannan ke nuna mana cewa dalilin halittar dan adam shine don ya bautawa Allah (SWT) ne kadai.

To menene bautar Allah (SWT)? Mutane da dama na daukar cewa bautar Allah (SWT) shine kayi sallah da zakka da azumi da kuma hajji. Wannan haka yake, amma ba wai bauta ta takaita da wadannan abubuwa ba ne; sun dai kasance ginshikai ne kurum. Saboda haka, bauta a iya cewa aikata wadannan abubuwa ne (ginshikai) kamar yadda Allah (SWT) yace da kuma tafikar da dukkan sauran al'amuran rayuwa cikin lura da horo da kuma hani na Allah (SWT). Domin idan muka diba wadannan ginshikai na bauta suna da kayyadajjen lokaci da ake yin su. Kaga kenan idan aka takaita ma'anar bauta da aikata su kadai zai zamana kamar waccan aya dake maganar bauta ba'a fahimce ta ba, tunda abinda take nunawa babu wani lokaci da dan'adam zai kasance (ya wajaba ya kasance) ba karkashin bautar Allah (SWT) yake ba.

No comments:

Post a Comment